TAMBAYA
SALAM menene banbancin maniyi da maziyi da wadiyi??
。
。
AMSA
BAN-BANCIN MANIYI-MAZIYI-DA KUMA WADIYI TARE DA
HUKUNCI
。
BANBANCIN-MANIYYI;-
→Maniyyin namiji: ruwa ne mai kauri FARI wanda yake fitowa
alokacin babbar sha'awa. kamar saduwa, ko wasa da farji,
Warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari,
Idan ya bushe kuma yana kamshi ruwan kwai.
→Maniyyi mace: ruwa ne tsinkakke, mai fatsi-fatsi, Wani
lokacin kuma yana zuwa FARI,yana fitowa lokacin babbar
sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo
juna lokacin da yake fitowa, za ta ji tsananin
sha'awa da dadi lokacin da ya fito, kuma warinsa yana kama
da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shi
ma yana kamshi ruwan kwai, sannan sha'awar macce zai yanke
bayan fitowarsa.
HUKUNCIN-MANIYYI shine: Idan ya fita ta dalilin Jin dadi dole
sai anyi wankan tsarki amma idan ya fita ta dalilin Wuya (kamar
harbin Kunama ko jan wutar lantarki dss) to baya wajabta
wanka sai dai tsarki.
BANBANCIN-MAZIYYI:-
MAZIYI Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar
sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna
wacce kakeso, ko matarka, ko kallon macce ko namijin da kike
sha'awa, haka kuma yana fitowa
yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya tafiyarda
sha'awa, kuma wani lokacin ba ma a sanin ya fito. An faninisa
domin ya tsaftace hanyar da maniyi zai bi Malamai suna cewa,
Maziyyi ya fi fitowa mata, fiye da maza.
HUKUNCIN-MIZIYI shine; A wanke al'aura gaba daya da kuma
Inda ya taba haka kuma Idan mutum na da alwala ya fito masa
to ya sake alwala.
BANBANCIN-WADIYYI:-
WADIYI Wani ruwa ne mai KAURI da yake fitowa a karshen
fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yi bahaya
a, yana fitowa ga wadanda ba suda aure, ko wadanda suka yi
nisa da mazansu ko matansu.
HUKUNCIN-WADIYI Shine; Hukuncinsu daya da Fitsari ana yin
tsarkinsa kamar yadda ake yin na fitsari.
Yana da Matukar kyau dukkan Musulmi ya san Wayannan
Banbance-Banbance da Hukuncinsu, Allah yayimana jagoranci.
Please share and Comment.
No comments:
Post a Comment
Comment