Leave a message

Breaking

Post Top Ad

| Latest News | Entertainment | Seince & Technology |Advertisement |Videos| Books | Love Quate & Others |

Thursday, 26 April 2018

TATSUNIYA GATANAN GATANAN KU (GONAR GIZO)

GATA NAN GATA NAN KU... Gizo ne dai, gizo ne dai yakasance rago malalaci baya aikin fari balle na baki, kullum sai dai yaci ya sha ya kwanta yai ta sharar barci. Abincin da suke ci ma matarsa koki ce ke siyo musu a kasuwa in takai tallan daddawa. To wannan lalaci na gizo yana damun koki tun tanahakuri dashi har ya fara kureta, kwanci tashi wata rana an wayi gari ana ta faman lafta ruwansama kamar da bakin kwarya, bayan an gama ruwa kowane manomi ya dauki kayan aiki ya tafigona amma gizo yana can a kwance abinsa yanata sharar barci.koki tazo ta ganshi sai haushi ya kasheta sai ta debo ruwa mai sanyi ta kwara masa; haba kan kace me ai tuni gizo ya tashi firgigi yana makyarkyata don tsoro. sai koki tace "tashi ka tafi gona shege kawai malalaci, kai dai wallahi kaji kunya" dakyar dakyar dai koki ta takura masa ya tashi, sai yace to dakata "zani gona amma da sharadi, a gaskiya sai kin soya min gyada (amaro) ina aiki ina ci". sai koki tace bakomai sai ta tashi ta soya mashi ta bashi da ruwa mai sanyia gora.Koda gizo ya isa gona sai yaje ya tayo igiyar kalgo yaje gindin wata katuwar bishiya mai sanyi ya daura lilo ya hau yana lilo yana rera waka yana kuma watsa soyayyar gyada a baki abinsa, haka yayi tayi har rana tayi sai ya sauko daga lilon sai ya share wuri a tushen bishiyar yakwanta yana ta sharar barci abinsa har bayan la'asar sannan ya dawo gida yana nishi wai shi sarkin noma. koki na ganinsa ta rugo da gudu tatarbeshi tana masa sannu da zuwa sannan ta bashi ruwa da abinci ya kara labtawa, sannan yazauna ya fara sharawa koki karya, har yana ce mata wai shi tunda yake bai taba noma irin na yau ba, ai ko sarkin noma bazai iya yin aikin daya maka a yau ba, koda koki taji haka sai ta buga guda tace "ahayye ayyururui lallai bana duk garin nan ba wanda zai fimu dibar hatsi, sannan taci gaba da zugashi.Haka dai kullum gizo yakeyi ita kuwa koki bata sani ba tana tsammanin abinda yake fada mata gaskiya ne.kwanci tashi har hatsin mutane ya fara nuna, har wasu sun fara kawo hatsi gida amma su gizo ba labari abin har ya fara damun koki.Wata rana gizo ya tafi gona kamar yadda ya saba sai yaga wani mutum a gona ya lafta huda,saboda tsiya irin ta gizo ko sannu bai mishi ba sai da ya bari mutumin ya tashi sai yaje ya tugo tafasa da yawa yazo duk ya dasasu a gonar mutumin nan. Koda ya dawo gida sai yace ma koki ta hau saman bishiya ta hango gonar gyadarsa, sai kuwa koki ta hau saman bishiyar dake tsakiyar gidansu sai yace mata "kinga gonata caaan" wato ya nuna mata gonar daya dasa tafasa, ai kuwa koki na ganin haka sai murna ta kasheta tana tsammanin cewa gonar gizo ce. Saboda murna koki har tana fadowa daga saman bishiyar, amma ko damuwa batayi ba, tana ta tsalle abinta tana cewa lallai bana zamu ci gyada wohoho.Kwanci tashi har manoma sun fara tsinko gyadarsu amma gizo wayam ba labari, in koki tace mishi suje gona gewaya su gani ko gyadar tayi sai ya rika cemata bata kosa ba tukun. Tofa da gizo dai yaga asirinsa zai tonu sai wata rana ya tafi gonar sarki sata, ya tugo gyada mai tarin yawa ya kaiwa koki yace wai daga gonarsa ya ciro. Wata rana yayan sarki sun zo gewaya sai sukaga anyi musu barna a gona ashe dama a lokacin gizo yana cikin gonar ya boye acikin wani kuttu basu ganshi ba. A tsiya irin ta gizo sai ya raya a ransa cewa bari ya basu tsoro sai ya shake murya ya fara rera wata waka yana cewa"Kuttu, kuttu, kuttu banban kuttu, kuttu maci yayayen sarki har sarkinma kansa"'haba koda yayan sarki sukaji wannan abu sai suka firgita sukace kafa me naci ban baki ba, suka ruga gida suka fadi gaban sarki suka bashi labarin abinda suka jiyo a gona.Sai sarki ya umurci wazirinsa da fadawa suje sugano ko menene a gonar. Ai kuwa nan da nan fadawa suka shirya suka hau dawaki aka garzaya sai gonar sarki, suna iso wa gizo ya gansu sai ya kara boyewa dakyau sai ya shake murya ya fara rera musu waka kamar haka:"Kuttu, kuttu, kuttu banban kuttu, kuttu maci fadawan sarki, kuttu maci wazirin sarki har sarkinma kansa"'haba koda su waziri sukaji wannan abu sai suka firgice suma kota kan dawakinsu ma basu biyo ba, ba abinda kake gani sai manyan riguna sun cika hanya ana shekar gudu, har rawanin waziri yana faduwa ai waziri ko kula rawanin bai yi ba. Sukaje gaban sarki suka fadi suna haki. Sarki ya hararesu yace yau ga kartin banza kawai wannan abin kunya har ina ace kamarku kuna gujewa dan karamin abu, to bari ni in tafi da kaina in ga ko menene.Sai sarki ya samu wasu fadawansu jarumai suka tafi, suna isa gonar sai gogannaka gizo ya kara boyewa cikin kuttu, to dama lokacin da suka isa gonar sarki bai sauka daga kan doki ba,sai ya umurci fadawansa da su shiga su kamo ko menene, nan da nan buja-buja suka fada gona; haba gizo yana ganin haka sai shake muryarsa fiye da kowanne lokaci sai ya fara waka"Kuttu, kuttu, kuttu banban kuttu, kuttu maci fadawan sarki har sarkinma kansa"'haba koda sarki yaji wannan murya mai ban tsoro ai bai san sa'adda ya fado daga kan dokinsa ba ya kwasa a guje bujum-bujum cikin babbar riga sarki yayi gudu kamar zai tashi sama, haka suma fadawan da yazo dasu ba wanda bai arce ba, da suka kusa da gari sai sarki yace su tsaya haka kar su shiga gari haka ayi musu dariya.Da suka isa fada sai sarki ya tara manyan fadawansa sukai shawara, daga karshe suka yanke shawarar kafa tarko na budurwar danko, wato za'ayi wata siffa ce ta budurwa da danko ta yadda duk wadda ya gani zaiyi tsammanin cewa budurwar gaske ce. Bayan an gama suranta budurwar danko sai akaje tsakiyar gonar aka aje. Koda gizo ya dawo sai ya tarar dabudurwa kyakkyawa a tsaye acikin gonar sai yace "wash tsuntsu daga sama gasasshe" sai ya tafi inda take sai yace "yar budurwa-budurwa ya kike?" yaji budurwa batace masa komai ba, ya gama duk maganganun da zaiyi amma batace masa uffan ba, sai yace shegiya mai girman kan tsiya ana magana kinaji kinki amsa min. Sai ya shareta da mari sai hannunsa ya makale, sai ya kara shareta da mari da hannun hagu sai shima ya makale. Sai yasa kafa ya haureta nan ma dai kafa ta makale, a haka sai da gizo ya manne ajikin budurwar danko tam-tam yayi yayi amma ya kasa bambarewa, yana cikin kici-kici sai ga fadawan sarki suka kamashi suka tafi dashi wajen sarki.Koda sarki yaga gitso cuku-cuku a jikin budurwar danko sai ya fashe da dariya har yana tuntsirewa, sai yace amma gizo ka cika lalatacce dama kaine ka shiga kuttu kake bamu tsoro haka? To zakaci gwafar ubaka yau, sarki yasa aka kai gizo bayan gari aka daureshi a karkashin wata bishiya aka tafi dauko dami-dami na bulala wadda za a zane gizo. Bayan fadawan sun tafi kenan sai ga wata kura tazo wucewa sai ta tambayeshi lafiya aka daureshi haka, sai gizo yace hmmm ke dan Allah ki tafi ki bani wuri ni kadai zanci. Sai kura ta tambayeshi me zaici sai yace hmm ai fadawan sarki suna nan sun tafi zasu kawo min nama soyayye na bijimin sa, kuma ni kadai zanci abina.To dama dai kun san halin kura wajen kwadayi nan take sai miyau ya fara zuba daga bakinta dalalala! sai ta roki gizo tace wai ta kwance shi, shi kuma ya daureta. Gizo yana jin haka sai ya fakaici idonta yayi dariya ya yarda takwance shi, shi kuma ya daureta. Shikenan Gizo ya tsira kenan sai ya ruga gida abinsa gun matarsa koki.Amma ita kuwa kura bayan fadawan sarki sun dawo da damin bulala tunda ta hangosu daga nesa ta fara fesa zawo, da suka iso inda take sai wani daga cikinsu yace laaaa! Kunga shegenya zama kura, sai wani kuma daga cikinsu yace ba kura ba ko zaki zai zama yau sai mun bugi banza. Sai kowa ya sauke damin bulala dake kanshi suka hau tsalawa kura bulala har sai da damin bulalan nan suka kusa karewa, sannan kura ta sami sa'a ta kubuce musu ta ruga cikin daji tana fetsa zawo. KURUNGUSSS! Kan dan bera!

No comments:

Post a Comment

Comment

Post Top Ad

Your Ad Spot
+widget
a