Kimiyya Da Fasaha
"YANDA WUTAR SOLAR KE YIN AIKII"
Biyo bayan bukatar wani dan uwa na ayi bayani kan yanda ake hada wutan solar ya sa mu rubuta muku wannan cikakkaken bayani kan hadawa da kuma aikin wutan solar.
Wutan solar dai duk inda ka ganshi, to abu mafi muhimmanci shine solar panel, wanda abu ne mai kiran gilashi wanda shike ke da fasahan da kan canza hasken rana zuwa wutan lantarki mai na'yin DC;kuma duk solar panel kwaya daya wanda shi aka fi anfani da shi a gidaje, kan zo ne da karfin wuta nau'yin DC 12V. Wanda kuma, dai dai karfin kowa, wani za ka gan shi da daya, wani biyu ,wani biyar wani goma---iya dai bukatar mutum da abin da zai yi da wutan.
Kasantuwar wuta nau'in DC baza mu iya anfani da shi kaman yanda yake da wutan batir din mota, muna bukatar na'ura wacce ake kira "inverter"don canza nau'in wutan daka DC zuwa AC. A aikace, bayan inverter ya canza wutan daka DC zuwa AC zamu iya anfani dashi kamar dai mun kunna janareto, amman don ijiyan wutan don anfanin dashi wani lokacin, muna bukatar batir wanda karanci na karamar mota duk da na mashin da makamantan su za su iya yi amman ba za su dade ba. Kamar dai shi solar panel din, batir din ma dole ya zama yana da karfin wuta nau'yin DC 12V, duk da akwai batir mai 24V ba za ka yawaita ganin shi ba don bama kowa ya san shi ba.
Abu na karshe wanda kuma shine mataki na biyu, shine na'ura mai kula da cajin batir don kar da karfin wuta ya lalata shi mai suna "charge controller" da turanci, kamar dai yanda kuke gani a hoton.
No comments:
Post a Comment
Comment