Leave a message

Breaking

Post Top Ad

| Latest News | Entertainment | Seince & Technology |Advertisement |Videos| Books | Love Quate & Others |

Saturday, 5 January 2019

Yanda Zaku Gyara "Memory Card" Dinku A Saukake.



YADDA ZAKA GYARA MEMORY CARD ɗin KA IDAN YA LALACE
Kimiyya Da Fasaha

Yan da ake gyara Memory Card ko Flash Dinka idan ya lalace ya yi (Currupt). Memory Card shi ne abu na biyu mafi soyuwa da Muhimmanci a cikin waya bayan layi (Sim Card). Mu kan ji ba dadi yayin da Memory Card dinmu ya lalace (Currupted), misali kana kan amfani da Memory Card dinka, kwatsam! Sai kaga ya nuna maka "Damaged SD Card" in kayi Format din a cikin wayar ya kiyi, in ma an sa a computer anyi format dinsa haka zai ta nuna maka koda kayi format din ba zai ci gaba da amfani ba.
A takaice dai Memory Card dinka ya lalace ka rasa komai na cikinsa, ka rasa shi kansa Memory Card din.
Abinda za'ayi magana a yau shi ne yanda zaka gyara Memory Card dinka a sauKake ba tare da kayi amfani da wani Software ba. Abubuwan da ake bukata kafin gyara Memory Card ko Flash:
1. Natsuwa: yana da kyau ka natsu sosai wajen gyara lalataccen Memory Card ko Flash dinka.
2. Lalataccen Memory Card tare da Card Reader waton gidan sa Memory Card din
3. Computer: Dole da ita za kayi aiki wajen gyara Memory Card din naka.
Da farko ka bude Coputer din sai ka danna alamar Windows din Computer, zai fito maka da shafuKan Computer din a kasa. Akwai wajen search sai ka rubuta "CMD" kana rubutawa zaka ga ya fito, sai ka budeshi inya bude sai ka rubuta “DISKPART” sai ka 5aba Enter Key na Computer.
Daga nan zai kai ka wani shafin, sai ka rubuta “ LIST DISK” sai ka danna Enter Key zai nuno maka Disk wato Memory din Computer din da kuma lalataccen.
Sai ka duba kaga wannene lalataccen a ciki, Disk 1 ne ko DisK 2 amma yawanci yafi zuwa a DisK 1, sai ka rubuta “SELECT DISK 1” sai ka taba Enter Key zai nuna maka DISKPART> DisK 1 is now selected sai ka sake rubuta “CLEAN” sai ka taba Enter Key DisKPart> Succeed Cleaning The Disk. Sai ka sake rubuta “CREATE PARTITION PRIMARY” sai ka tba Enter Key, zai nuno maka DISKPART> Succeed Creating In The Specified Partition
Sai ka rubuta “ACTIVE” sai ka taba Enter Key zai nuna maka DISKPART> Marked The Current Partition as Active sai ka rubuta “SELECT PARTITION 1” sai ka taba Enter Key zai nuna maka, Partition 1 is now The Selected Partition sai ka sake rubuta “FORMAT FS=FAT32” sai ka taba Enter Key daga nan zai fara Format zaka ga ya sama 0% to Complete. A haka a hankali har sai ya kai 100%. Ka tabbatar kayi shi kamar yanda yake.

No comments:

Post a Comment

Comment

Post Top Ad

Your Ad Spot
+widget
a