TAMBAYATA
Assalamu Alaikum tanbayata itace ya ake gane."kabli da ba'adi".Kuma ya ake gyara su.?
。
。
AMSA
Da farko mu sani cewar duk abinda yake farillane
a sallah kuma akabarshi to kabaliyyah ko ba’adiyyah
bata gyarashi, to haka hukuncin yake a salloli na nafila?.
Haka kuma duk abinda mustahabbine a sallah to shima
ba’a yi masa kabaliyyah ko ba’adiyyah.
Dukkan rafkannuwa da aka yi ta a lokacin da ake ramuwar
sallah to hukuncinta kamar sallar da ake yenta ne a cikin
lokaci, kenan ba banbanci da sallolin ramuwa da kuma
wadanda ake yinsu cikin lokaci.
Yin rafkannuwa a sallar nafila hukuncinsa kamar yin
ranfannuwa ne a sallolin farilla in banda mas’aloli guda
shida ananne nafila ta banbanta da farilla, sune kuma
kamar haka:
(1) Karatun Fatiha: Duk wanda ya manta da karatun fatiha
a sallar nafila bai tunaba sai bayan ya yi ruku’u sannan
ya tuna to anan zai ci gaba da sallar shine sai bayan ya
kammala ya yi kabaliyyah, sabanin sallar farilla da zai cire
wannan raka’ar ya kawo wata makwafinta sannan ya yi
ba’adiyyah idan ba’a biyun farko bane, ko kabaliyyah
idan hakan ya farune a biyun farko na farilla.
(2) Karatun Sura.
(3) Bayyanawa.
(4) Sirrantawa.
Idan mutum ya manta karatun sura bayan fatiha a cikin
sallar nafila, ko kuma ya bayyana a inda ake asurtawa ko
ya sirranta a inda ake bayyanawa kuma bai tunaba sai
bayan da ya yi ruku’i to zai ci gaba da sallar shine, amma
duka a cikin nafila to babu komai akansa, wato ba
kabaliyyah kuma ba ba’adiyyah, sabanin inda sallar
farilla ce.
(5) Tashi Zuwa Raka’a Ta Uku: Dun wanda ya kammala
raka’o’I biyu a sallar na fila sai bai zaunaba ya mike
zuwa raka’a ta uku to idan ya tuna kafin ya kulla ruku’u
to anan zai dawo ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama,
sannan kuma ya yi ba’adiyyah, amma har idan ya kulla
raka’a ta uku to zai ci gabane da sallar sai ya karat a
zama raka’o’I hudu sannan sai ya yi kabaliyyah,
sabanin sallar farilla.
(6) Manta Rukuni: Duk wanda ya manta rukuni a sallar
nafila kamar ruku’i ko sujjada kuma bai tuna ba har ya yi
sallama kuma abin ma ya yi tsawo to anan ba zai sake
sallar ba, sabanin sallar farilla, domin inda farillace to da
zai sake sallarne har abada .
Kammalawa: Wadannan sune wuraren da aka dan sami
banbanci tsakanin salloli na farilla da salloli na nafila akan
abinda ya shafi hukunce-hukuncen rafkannuwa, da fatan
Allah yasa ya anfanar da mu.
Please Share and Comment
No comments:
Post a Comment
Comment