Gaskiya Sayyiduna Abubakrin (ra) yayi Qokari.
Domin azamanin Khalifancinsa ne aka samu
dubunnan mutane duk sunyi ridda tunda
sukaji labarin wafatin Manzon Allah (saww).
Musamman larabawan Qauye da na Qananan
garuruwa, da kuma sauran Qabilu. Har sai da
ya zamto aduk cikin daular Musulunci babu
wajen da zaka samu jama'ar Musulmi zalla
sai dai garuruwa 3 kadai. Wato MADEENA,
MAKKAH da TA'IF. ...
Daga cikin wadannan Qabilun akwai wadanda
suka koma bautar gumakansu na da chan.
Akwai kuma wadanda sukayi Qaryar cewa wai
su ma Annabawa ne. Kamar irinsu
Musaylamah da Aswadul Unsiy, da Tulaiha da
Sajjaahu.
Akwai wadanda kuma suke jayayya da wani
bangare na Musuluncin. Kamar Zakkah, akwai
wadanda suka dena bayar da ita.
Sannan akwai kuma wadanda suka bi
wadancan Annabawan Qaryan.
Amma dukkansu sai da Sayyiduna Abubakrin
ya yakesu kuma yaci nasarar dawowa da
wasunsu kan hanya.
Wasu kuma aka kashesu akan haka. Wasu
kuma aka samu nasarar korarsu daga yankin
larabawa baki daya.
Amma fa duk wannan katafaren bala'in da ya
bullo, Sayyiduna Abubakrin yayi maganin
abun ne acikin Shekara Uku da 'yan watannin
da yayi yana Khalifanci.
Da farko dai ya fara tura rundunar Usamatu
bn Zaid (ra) wacce dama Annabi (saww) ne
yayi umurnin su tafi. Amma jin labarin
Rasuwarsa ya dakatar dasu.
Bayan sunje sunyi yakin sunyi nasara sun
dawo sun huta, sai Sayyiduna Abubakrin (ra)
ya Qulla rundunoni Goma sha daya na sojojin
Musulunci domin yaki da masu ridda.
Insha Allahu zamu kawo muku sunayen
Kwamandodin kowacce runduna da kuma
wajen da aka tura su..
Ya Allah ka Qara yardarka abisa Sayyiduna
Abubakrin Babban Khalifan Manzon Allah
(saww).
No comments:
Post a Comment
Comment