YANDA AKE SAMAR DA WUTAN LANTARKI TA HANYAR ANFANI DA RUWA
Kimiyya Da Fasaha
Kaman yanda muke iya gani, hoto daya zane ne na yanda ake anfani da karfin gangarowan ruwa da gudu wajen juya na'uran janareton da kan samar da wutan lantarki. Hoton na biyu kuma zahirin yanda ruwan kan zuba ne kuma tare da juya janaretocin da aka kafa don samar da lantarki, duk da baza mu iya ganin janaretocin ba. To amman dai haka abin yake.
A hoton farko, alaman ruwa ne ake gani me launin shudi(blue). Sannan ga inda yake gangarowa nan da gudu, daga tudu zuwa kwari. Daka kasa kuma, za mu iya ganin wani abu mai launin ja, to wannan ne janareton ,kuma ruwan kan juya shi da gudu. Wannan juyawa ne kan sa janareton bayar da wuta, kaman dai yanda a gidajenmu mu ke samun wuta ta hanyan gudu da janareton mu ke yi idan muka zuba man petir.
Irin haka ne a najeriya ake samun wutan lantarki daga wurare kaman su kainji da sauran madatsun ruwa
No comments:
Post a Comment
Comment