BANGARORI DABAN DABAN NA INJIN MOTA DA AIKIN SU
Kimiyya Da Fasaha
GANGAN JIKIN INJI (EGINE BLOCK)
Idan muka dubi wannan hoton, abu na farko daga sama ta hannun hagu, shi ne gangan jikin injin din wanda ake kira "egine block" da Ingilishi. Idan muka dube shi da kyau zamu iya ganin ramuka manya manya a samanshi har guda shida. Da kuma wa'yansu kanana. Kuma duk wani abu da ke cikin hoto yana da mazauninshi a jikin gangan jikin injin din. Manyan ramukan da ke saman injin din ana kiransu silinda(cylinder da ingilishi). Yawa silinda ke nuna karfin da injin din ke da shi. Kuma na da matukar muhimanci mu iya sanin yawan silindan da ko wane injin, walau na babur ko na mota karama da mota babba har ma zuwa jirgin kasa da na ruwa da ma na sama, kan zo dashi. Idan mun dauki injin babur da na karamin janareta, yawanci sukan zo ne da silinda daya ko biyu. Injin karamin mota kan zo ne da silinda hudu a yawanci lokuta. Injin tirela da sauran manya manyan motoci kan zo ne da yawan silinda da ya kama daga shida zuwa takwas da ma fiye da haka. Kuma yawanshi, girma da fadi ke bayar da kamannin karfin da injin din ke da shi.
SILINDA(CYLINDER)
Shine abu na biyu a cikin hoton ta hannun dama. Silinda, a lura, bangare biyu gare shi. Bangaren da muka tattauna a kan shi a bayanin mu na dama, ramin silindan ne dake jikin injin din. Amman bayan wannan akwai kwaskwaro silinda din da kan shiga ya zauna. Kuma ina gani dalilin da yasa aka yi shi haka maimakon ya zama na dun dun dun ba se an rika cire shi ba, shine don bada daman canza shi, tunda ya kan samu matsala har ma a bukaci canza shi.
Lamari mafi muhimmanci a injin shine konewan man fetir(combustion) kuma wannan na faruwa ne a cikin silinda ta sama. A lokacin da man fetir hade da iska daga wajen injin din suka shiga cikin silinda ta sama, plug(spark plug) kuma ya kysta musu wuta, to hakan kan haifar da konewan me hade da hayaki da iska mai karfi. Wannan karfi na iskan ne ke tura piston( abu na farko a saman hoton ta hannun dama) wanda ke cikin silindan da karfi, wanda wannan turawan sama da kasa ne da kan faru a cikin ko wane silinda kan rika juya karanshaf(crank
shaft) da gudu. Haka dai wannan juyawa zai ci gaba matukar mai da iska suka ci gaba da shiga cikin silinda.
PISTON
Wannan ne abu na farko a saman hoton ta hannun dama.Kuma abun da kan rike shi a cikin injin din shine karfen da ake kira "connecting rod"( karfe me hadawa). Kuma wannan karfe me hadawa shinecabu na biyu a dai saman hoton ta hannun hagu. Kuma in a lura za a ga wani rami ko huji a jikinsa, ta nan ne ake hada piston din da karfen kaman yanda a jikin piston din shima akwai kwatankwacin wannan rami. Shi yasa in ka taba ganin piston wanda aka cire zaka ga saman shi bakin kirin. Wannan dole ne, don duk wani man fetir da aka sa a mota ko janareto kan rika konewa ne kadan kadan a saman piston din har se ya kare sannan wannan konewan kan tsaya.
RING(ZOBE)
Idan mun kalli hoton daga sama kuma abu na uku, za mu ga karfe mai kama da zobe, wanda hakan ya bashi sunnan zobe amman ba irin na sawa a hannu ba. Wannan zoben akan saka shi ne a jikin piston. Zamu iya ganin wa'yansu zane zane ko layika a jikin piston din, nan ne inda zoben kan zauna. Babban anfanin shi shine toshe yar hanya da ke tsakanin piston da kuma bangon silinda. Wanda in bashi , hayaki ze dinga wucewa daga saman piston din zuwa kasan ingin din. Wanda wannan ze kawo cikas ga aikin injin din koma hana shi aiki gaba daya. Don haka, aiki ring wato zobe shin hana hayaki da iska mai karfi da kan faru a saman silinda wucewa kasan silindan. Kuma zamu iya ganinsu kala daban daban, kowanne na da takamai man aikin shi.
CONNECTING ROD(KARFE ME HADAWA)
Shine abu na biyu daga saman hoton ta hannun hagu.Kuma kaman yanda muka fada, shine ke rike da piston a cikin silinda ta sama, sannan krankshaft ta kasa. Idan mun lura za mu ga yana da ramuka biyu: daya karami daya babba. Karamin ta nan ake daure piston, babban kuma ta nan ne ake hada krankshaft da piston din. Kar kuma a manta, mun fadi cewan dannawa da pistin kanyi sama da kasa ne kan rika juya krankshaft, duba da siffan da krankshaft din ke dashi. Kuma hade yake da wa'yansu kananan abubuwa da kan taimaka wajen daura shi ko kwance shi. Kuma akwai bukatan a san su dalla dalla.
CRANKSHAFT(KRANKSHAFT)
Daka jikin hoton , shine abu na farko ta hannun dama, kuma a tsakiyan hoton. Shine dogon karfe mai lankwashe lankwashe, kuma shi ne ke ainihin juya gabadayan injin din. Kuma dukkan wani piston daure yake da jikin krankshaft din, komai yawansu, tunda su ne ke haifar da karfin da ke juya krankshaft din shi kuma krankshaft ya juya gabadayan motan ko janareton ko ma duk wani abun da ake son juyawa.
VALVE(KARFE MAI MALFA)
Wannan shine abu na kusa da krankshaft, wato abu na biyu a tsakiyan hoton daga bangaren dama na hoton. Babban aikin karfe me malfa(valve) shine bayar da dama don fetir da iska su shiga cikin cikin silinda don konewa, da kuma bayar da dama ga hayakin konewa don fita zuwa salansa. Malfan da karfen ke dashi shi ne kofar da man fetir da kuma hayaki ke bi. Ma'ana dai, akwai karfe mai malfa akalla guda biyu a saman kowane silinda, daya don shigan fetir hade da iska daya kuma don fitan hayaki. Kuma yanayin wannan aikin ne hade da spring da za a iya ganinsu tare.
CAMSHAFT(KAMSHAFT)
Shine abu na biyu daga kasan hoton, kuma aikin shi shine gudanar da karfe me malfa. A lokacin da injin din ke juyawa, shima camshaft kan rika juyawa da gudu yana kuma budewa da rufe karfe me malfa. Abu ne me matukar sarkakiya, domin kaman yanda krankshaft ya dogara da piston domin juyashi, haka nan duk wani valve ko karfe mai malfa ya dogara ga camshaft domin budewa da rufewa. Amman mu'amulla dashi ze matukar bayar da kyakyawan fahimta game da shi.
CYLINDER HEAD(KAN SILINDA)
Wannan shine na farkon ta hannun hagu daka kasan hoton. Kaman yanda za'a iya lura, shine karfe mafi girma bayan gangan jikin injin din. Kuma cikin abubuwan da ke zama a kan shi sun hada da: camshaft, karfe me malfa, plug(idan injin me aiki da man fetir ne ba diesel ba), rocker arm assembly(wa'yansu karafa da ke hade da camshaft) sai kuma karfen da kan amshi hayakin da ke futowa daga saman injin din wanda ake kira "exhaust manifold" da ingilishi.
HEAD GASKET(MATOSHIN ISKAN SAMAN SILINDA)
Shine abu na farko ta hannun dama ta kasan hoton, kuma anfani shine hana iska shiga ko fita daga cikin injin din. Shi dai abu ne da aka yishi da jikin da ba karfe bane amman yana da matukar jure tsananin zafi wanda injin kan haifar lokacin da yake aiki. Yana kuma zama ne tsakaning kan Silinda da gangan jikin injin din. Kuma akwai bukatar duk sanda akayi wani aikin da ya kai ga an sauke saman silinda to a saka sabon matoshin iskan saman silindan.
GEAR BOX(AKWATIN SARRAFA GUDUN INJIN)
Duk da babu shi a cikin hoton, amman muhimmancin shi na da yawan da dole muyi bayaninshi. Shidai wani katon gida ne na karfe wanda ya kunshi fayafayai daban daban wa'yanda kuma kowannensu na matsayin wani takaitaccen gudu ne da injin din ake bukatan ya bayar. Wannan ne yasa ake kiranshi da suna AKWATIN SARRAFA GUDU wato gear box da ingilishi. A sanda muke sakawa ko canza gudu a motarmu, wannan canzawa duk da muna yin shi ne da hannu, sako ne kawai muke aikawa zuwa ga akwatin sarrafa gudu.
STATA DA ALTANETO(STARTER AND ALTERNATOR)
Dukkan su hade sukkan rika juyawa a lokacin da injin din ke guru ko aiki ta hanya anfani belt a yawancin lokuta. Yayin da aikin stata shine juya injin a lokacin tayar da shi, altaneto kuma aikin sa shine samar da wutan lantarki ga dukkan jikin motan domin cajin batir, anfani da radio da sauran kayan jikin motan da ke bukatar lantarki. Kuma wani abin lura shine, alterneto na mota yawancin yakan zo ne da wutan lantarki na'in DC kuma tsakanin 14.5 volt ko 29 volt ko abin da yai kusa da haka don iya caza batir din motan da 12 volt ko 24 volt ya kan kasance na karfin wuta. Stata dai anfanin sa shine samar da karfin juyawan da kan juya injin din kaman yanda muka bayyana, kuma wutan da yake anfani da shi kan zo ne daga batir din motan. Dukkanin su , stata da lataneto sun kunshi wayan koil ne a cikin su. Yayin da stata ke amsar wuta, shi kuma altaneto bayar da wuta yakeyi.
Ga masu sha'awan zamowa masu gyran inji me aiki da man fetir ko diesel, to babban shawara shine, bayan karatu da fahimtar kowane bangare na injin, to mutum ya samu wajen kanikawan injin mafi kusa da shi don ci gaba da neman kwarewa. Don wannan jawabi sai dai ya daura mu kan hanya.
No comments:
Post a Comment
Comment