Kimiyya Da Fasaha
WALDA
1.MENE NE WALDA?
2. WALDA IRI NAWA NE?
3. YA AKE YIN ANFANI DA INJIN WALDA?
4. WA'YANSU KAYAYYAKI NE AKE BUKATA DON ZAMOWA ME SANA'AN WALDA?
1. MENE NE WALDA?Walda shi ne hada karfe da karfe ta hanyan anfani da zafin wuta wanda ke da karfin zafin da kan narkar da karfen. Ko wane nau'in karfe( Alminium,bakin karfe da farin karfe, copper, nickel, zinc, dalma da sauran su) za a iya yin walda a jikinsa matukar dai an cika sharrudan da ake bukata.A ma'anance dai, hatta hada roba da roba da duk wani abu da ake iya hada shi ta wannan hanyar sunan shi walda.
Walda na da matukar tasiri a rayuwan mu na yau da kullum, kuma kirkiro walda da dan adam ya yi ya sauya gabadayan yanda muke rayuwa da mu'amulla da karafa da kuma muhallinmu.
Idan kuwa ana maganan kera wuraren rayuwa ko kasuwanci, to abun da zai iya dara walda to kila shi ne siminti da yashi don yanda ake hadawa da kuma jona bulo da bulo . Hakan yasa babu alamun za a samu wani lokaci da dan adam zai iya daina bukatan walda a rayuwanshi.
2. WALDA IRI NAWA NE?
Mafi yawancin nau'kan waldan da muka sani muka kuma fi sabawa da su iri biyu ne:waldan tsinke da kuma walda da iskan gas mai suna "Oxy-acetylene".
2.1 WALDAN TSINKE
Waldan tsinke( stick welding/arc welding) ana aiwatar da shine ne ta hanyar anfani da tartsatsin wutan lantarki(arc), Wanda hakan ya sa ake kiran sa da Arc Welding. Kuma wannan ne nau'in walda da muka fi sani kuma muka fi sabawa da shi. Hakan kuma na da alaka ne da saukin shi da kuma rashin tsadan shi da ma kuma rashin yawan kayan aiwatar da shi.Don da zaran an hada injin din da wutan lantarki to sai yin walda kawai. Wanda shi kadai ke da irin wannan saukin duk da akwai hatsarin mu'amulla da wutan lantarki, amman idan aka bi matakan da suka dace wannan ba abun damuwa bane.
Waldan tsinke kan haifar da zafin wuta da ya kama daga 3,000°C zuwa 20,000°C, wanda hakan ke nufin babu wani nau'in karfe a duniyan nan da bazai narke ba a wannan yanayin na tsananin zafi.
A lokacin da waldan tsinke ke gudana, ba dukkan narkakken wajen da ake yin waldan ne karfe ba, akwai kumfa(slag) wanda sinadari ne dake a jikin tsinken waldan wanda kan taimaka wajen narkewan karfen jikin tsinken. Kuma a ido zaka iya yi mishi fahimtar karfe amman bashi da karfin karfe. kuma bayan cire tsinken da kuma hucewan inda akai waldan, akan rika dukan saman waldan da karamin guduma don kawar da shi kumfan da kuma ganin walda yayi ko bai yi ba. Idan waldadden karfen bai rufe dukkanin inda ake bukata ba,to sai a sake yin walda har sai an cimma adadin girman wanldan da ake bukata.
2.2 WALDA DA ISKAN GAS
A Wannan nau'in na walda, iskan gas na oxygen tare da na acetylene kan kan haifar da zafi wuta wanda yakai 3500°C na ma'aunin zafi sa'ilin da aka kysta musu wuta.
Akwai wurare da dama da akan yi anfani da irin wannan walda, ciki kuwa shine masu gyara ko kanikancin mota, masu yankan manyan karafa da sauran wa'yansu wuraren na yau da kullum.
Duba da cewan zafin da bakin karfe kan bukata domin narkewa kimanin 1530°C ne na ma'aunin zafi, wannan na nufin a ma'anance oxy-acetylene na da zafi sama da nikki biyu na zafin da zai narkar da bakin karfe. Wannan ke nufin zai iya yin waldan karfe da ma na aluminum, copper, brass da makamantansu.
Yanda zaka gane walda gas daga sauran nau'ikan walda shine ka ga dogayen gidan gas na karfe guda biyu, daya na oxygen daya kuma acetylene.
Sannan domin kariya daga hatsarin tashin wuta, yana da kyau a samu gidan iska na uku wanda ke dauke da sinadarin iskan kashe wuta na "Carbon-Dioxide" (CO2). A kuma dukkanin inda za aiwatar da walda ko wani iri ne, duba da walda ya kunshi wuta me tsananin zafi, akwai bukatan ijiye Sinadarin iskan kashe wuta na Carbon-Dioxide a kusa.
Sai dai kuma, yin walda ta hanyar anfani da tartsatsin wutan lantarki ko kuma waldan tsinke shine nau'in waldan da muka fi sani kuma shine yau aka fi anfani da shi don kiran ababe daban daban da muke rayuwa da su kaman babban kofar gida(gate), kofa da tagar dakinmu ko kuma na shagon yin san'a, tankin ijiya ko kuma na safaran man fetir da kanazir da ruwa , kujeran zama na gida ko na makaranata, abubuwan dai basu kirguwa. Wannan kuma na da alakane da saukin da hada kayan waldan tsinke ke dashi da ma kuma rashin tsadan shi. Kuma ko da inda babu wutan lantarki za a iya anfani da janareta babba don aiwatar da shi.
2.3 SAURAN NAU'IKAN WALDA
Bayan wa'yannan nau'ikan walda biyu da muka ce anfi yin anfani da su, ci gaban da aka samu a fannonin kimiyya da fasaha ya haifar da wa'yansu nau'ikan walda daban daban da
ake anfani da su a fannonin kere kere na musamman. Hakan yasa yau muke da nau'ikan walda kaman na MIG da TIG da Electron Beam da kuma Laser.
MIG(Metal Inert Gas) da TIG(Tungsten Inert Gas) suna da siffofi kusan iri daya:dukkaninsu suna afani ne da tartsatsin wutan lantarki tare da kuma iskan gas a lokaci daya. Wato dai, hanyoyi ne ko kuma nau'ikan walda ne da kan hada siffofin walda iri biyun da muka tattauna akai, waldan gas da na tsinke ko kuma tartsatsin lantarki. Amman a wannan nau'in na walda, a lokacin da tartsatsin lantarkin ke aiwatar da waldan, gas din shi kuma kan rika kewaye inda walda ke faruwa ne a matsayin kariya(shieldin
g). Wanda hakan kan haifar da kyakkyawan walda fiye da wanda za a iya samu inda walda tartsatsin wutan lantarki ne kawai ko kuma waldan gas ne kawai.
i. BANBANCIN MIG da TIG
A bangaren waldan MIG, siririn karfe dake nannade a jikin injin kan rika shiga inda ake yin waldan do samar da Karin narkakken karfen da za'a hade wajen da ake bukatan yin waldan.
A waldan TIG kuma, zafin tartsatsin wutan ne wanda iskan gas kan kewaye kan rika yin waldan ba tare da wani Karin karfe, ba kaman yanda yake da waldan MIG ba.
Babban abin da ya banbanta wa'yannan nau'ikan walda shi ne, idan ana bukatan yin walda ga karfe mai kauri to MIG ne yafi dacewa, duba da cewan ya kunshi nannadaden karfen da kan rika kara ma walda karfi.Idan kuma ana bukatan walda a karfe siriri mara kauri ne to waldan TIG yafi dacewa duba da cewan bashi da wani karin karfe a wurin da ake yin waldan.
ii. To Wannene Yafi Tsakanin waldan TIG Da Na MIG?
Ya danganta ne da yanayin karfen da ake son yin waldan akai, yaya girma da kaurin shi yake?
Idan dai karfen na da kauri to MIG zai fi dacewa. Idan kuma karfen siriri ne to TIG zai fi dacewa. MIG kan rika shigar da karfe siriri a tsakiyan inda ake yin waldan don waldan yayi kauri, amman TIG bashi da irin wannan karin karfen.
3. YAYA AKE ANFANI DA INJIN WALDA?
Babban abin da ke cikin injin walda mai anfani da wutan lantarki shine transformer.Kuma babban anfanin duk wani transformer babba ko kuma karami, shine ya canza karfin da wutan lantarkin ke da shi, wajen rage shi ko kuma ya kara masa karfi.
Dan haka anfanin da transformer ke yi a jikin injin walda shine rage karfin da wutan da lantarkin ke da shi daga kimanin 230V zuwa kimanin 20V, ko 50V ko kuma 100V na karfin wutan lantarki. Kuma kowane ajin karfin wutan na mazaunin wani adadi ne na karfin waldan da injin waldan kan baya, kuma za'a iya rage shi ko kuma kara shi idan an bukachi hakan.
Kaman kuma duk wata na'ura mai anfani da wutan lantarki, injin walda nada wajen da ake hada wayan wutan lantarki(input), kuma idan aka duba jikin injin da kyau za'a ga hakan. Haka nan kuma , akwai wajen fitan lantarki(output), wanda ta nan ne za a hada asalin wayan da za ja zuwa jikin inda za ai waldan.
3.1 YANDA TARTSATSIN LANTARKI KANYI WALDA
Misalin yanda wannan wutan da aka rage ma karfi daga 230V zuwa 60V kan yi walda,shine misalin yanda idan wayan wutan lantarki baki da kuma jan kan yi tartsatsi ida suka hadu da juna. Sai dai, yayin da haduwan ja da bakin waya(positive and negative) a wuta mai karfin 230V zai haifar da konewar waya nan take kuma ma yayi barna, hakan baya faruwa idan karfin wutan ya ragu zuwa 20V ko kuma 60V Sai dai duk da haka akwai hatsari idan ba a raba su da sauri ba, don injin kan kone a irin wannan yanayin.
Kuma mukan samu aiwatar da walda ne wajen yi anfani da tsinken walda(electrode) wanda ke dauke da sinadarin da kan haifar da tsananin zafin wutan da kan narkar da karfe nan take. Kuma karfen da ke tsakiyan jikin tsinken waldan ne hade kuma da na abin da ake yin waldan akai kan bayar da ruwan karfen da kan hada karfe da karfe.
Sa'anan, kaman yanda wayan wuta kwaya daya baya iya yin tartsatsi har sai idan ya hadu da waya na biyu,haka nan ma waya daya na injin walda ba zai iya yin walda ba har sai an samu waya na biyu, tunda mu ce tartsatsin wutan lantarkin ne kan sa tsinken waldan ya narke kuma ayi walda.
3.2 WALDA DA ISKAN GAS NA OXY-ACETYLENE
Akan dai yi anfani ne da nau'ikan °gas guda biyo wajen yin walda: daya iskan Oxygen dayan kuma na Acetylene, hakan yasa ake ma wannan nau'in walda da "oxy-acetylene welding'( waldan oxy-acetylene)a takaice. Dukkanin wa'yanan iskokin kuma suna cikin gidan iska ne, wato silindan. Kuma haduwan way'anan iskoki guda biyu da kuma cinna musu wuta a tare kan haifar da karfin wuta mai zafin kimanin dubu uku da dari biyar(3500°C) na ma'unin zai na celsius(selshius) ko kuma 6332°F a ma'aunin Fahrenheit.Wanda wannan ya isa ya narkar da duk wani nau'in karfe.
4. WA'YANSU KAYAYYAKI NE AKE BUKATA DOMIN ZAMOWA MAI SANA'AN WALDA?
Akwai dai jerin kayayyaki daban daban da mai son yin sana'an walda zai bukata kaman haka:
•WUTAN LANTARKI.
• INJIN WALDA.
• INJIN YANKA KARFE.
•ZARTO NAU'IN DA AKE YANKA KARFE.
• TAPE/MA'AUNI.
• GUDUMA BABBA DA KARAMI.
. BAKIN GILASHI.
•HULAN YIN WALDA MAI HADE DA GILASHI
•SAFAN HANNU NA FATA KO NA AUDUGA.
• TAKALMI SAU CIKI KUMA MAI KIBA.
•RIGA DA WANDO WANDA AKAYI DA AUDUGA MAIMAKON NA ROBA.
No comments:
Post a Comment
Comment