Leave a message

Breaking

Post Top Ad

| Latest News | Entertainment | Seince & Technology |Advertisement |Videos| Books | Love Quate & Others |

Wednesday, 9 January 2019

YANDA ISKA KE SAMARDA WUTAR LANTARKI


Science & Technology.
BAYANI GAMEDA YADDA ISKA KE SAMAR DA WUTAN LANTARKI.
Babu shakka iska abune mai Qarfin
gaske tayadda duk girman abu, kuma
duk nauyin abu babu shakka baiyi wa
iska nauyi kuma baiyi mata girma.
Babu shakka idan akasami turbine
( turbine abune wanda ba komi bane
acikinsa illa wayar coil dakuma
magnetor aciki, wanda idan ana juya
wannan coil din yana fitar da wutan
lantarki mai Qarfin Gaske) . Idan aka
sami wannan engine turbine dana
muku bayani akan daurashi acikin
dogon pole a wajajen da ake samun
iska yana yawan kadawa. Yawanci
akan sami waje mai tudu hakannan ,
kamar tsau nuka ko kan tudun sai
akafa pole mai tsayin gaske. wanda
tsayinsa yakai kamar tsayin antenna
na service din mtn da glo da dai
sauransu. Bayan ansaka wannan pole
din ankafashi sai kuma azo adaura
wannan turbine din ajikin pole din
acan saman pole din, akan daureshi
tayadda bazai fado ba.
Shi wannan turbine din yanada
propellors dazaka gani ajikinsa,
wannan farfelun suna hade ne da
jikin coil din dake cikin turbine din .
Daga lokacin da iska yafara juya
wannan farfelun to babu shakka
zakaga ansami wutan lantarki daga
cikin wannan turbine din. yawanci
anayi masa hikima guda daya. Akan
sami baturan mota manya manya
masu Qarfi sosai.
Idan wannan
enginge turbine yana juyawa toyakan
fitarda wutan lantarki wanda zaiyi
charging wannan manyan baturan
motar, amfanin hakan shine, koda
babu iska to su baturan zasu bada
wutan lantarki, shi wannan engine
turbine zakagansa kamar wani dan
karami, amma idan kazo kusa dashi
babu shakka yanada girma kamar daki
guda ne. domin engine turbine guda
daya zai iya bawa anguwanku ko
kuma rabin anguwanku wuta mai
Qarfi. Wanda zaku iya kunna fankanku
da tv dinku, wanda zakuyi iya kunna
heaters da dutsen guga agidajenku
batareda wani matsala ba.
idan ma
akauye ne akasaka wannan turbine
babu shakka zai iya daukan garin
yabasu wuta mai qarfin gaske.
amma karku manta cewa shi wannan
hanyan da ake amfani da iska wajen
samun wuta ana kiransa da suna
"wind power"
Please Share And Comment.

No comments:

Post a Comment

Comment

Post Top Ad

Your Ad Spot
+widget
a