Science And Technology
CIKAKKEN BAYANI A KAN
Kwayar Cutar Kwamfuta
(Computer Virus)
.
Gabatarwa
Daga wannan mako in Allah Ya yarda, zamu fara
bayanai kan manyan matsalolin da ke damun
kwamfuta da masu amfani da ita a wannan
zamani da muke musamman. Kamar dai yadda
dan Adam yake ne; yana da damuwoyi da dama
da ke masa kaidi wajen tafiyar da rayuwa
ingantacciya kuma cikin sauki. Haka na’urar
kwamfuta take; akwai matsaloli da ke mata
karan-tsaye wajen gudanar da ayyukan da aka
kera ta don yin su, cikin sauki. Wadannan
matsaloli suna da yawa, amma zamu dauki
wadanda suka shafi lafiyar ta da kwakwalwanta
ne kadai, don su ne manyan matsalolin da suka
fi kowanne tasiri wajen dama mata lissafi,
musamman cikin wannan zamani da aka samu
kwararru kan ilimin ta, birjik a duniya. Kamar
yadda taken wannan kasida ya nuna, zamu yi
bayani ne kan kwayoyin cututtukan da ke damun
na’urar kwamfuta a yau; daga ina suke; ta yaya
suke shiga jikin ta har su kai ga kwakwalwa;
mene alamun da ke nuna cewa kwamfuta ta
kamu da irin wadannan cututtuka masu sanya
ta zazzabi mai tsanani, a wasu lokuta ma su
hana ta sakat har su kai ta ga sumewa? Abin
da muka tanada kenan a yau. Mako mai zuwa
zamu kawo bayanai kan wadanda ke da alhakin
kirkiran wadannan cututtuka da kuma manufofin
su. Mu kuma ji bayanai kan hanyoyin da su suke
bi wajen yada wadannan cututtuka. Daga karshe
kuma masu karatu su samu bayanai kan
hanyoyin magance ire-iren wadannan matsaloli.
A kasance tare da mu.
Computer Virus: Ma’ana da Asali
Idan aka ce Computer Virus, a turance, ana nufin
kwayoyin cutar da ke haddasa ma kwamfuta
matsaloli ne na rashin lafiya; ko su rinka aikin
liken asiri a cikin ta, tare da aika ma marubucin
su bayanai, ko su sauya mata bayanan da take
dauke dasu, ko su goge su, ko kuma a wasu
lokutan ma, su sumar da ita. Su wadannan
kwayoyin cuta ba wasu abubuwa bane face
bayanai da ke kumshe da haruffa ko lambobi da
aka rubuta su ta amfani da kwarewar gina
manhajar kwamfuta, watau Programming
Language. Wadannan jakunkunan bayanai na
dauke ne da umarni da marubucin su ke ba
kwamfuta. Don haka da zaran sun shigi
kwamfuta, to ba abinda ya rage mata sai bin
umarnin da ke cikin su. Suna samuwa ne ta
hanyoyi uku; ko dai ya zama bayanai ne zalla da
aka taskance su cikin jakar adana bayanai. A
turancin kwamfuta ana kiran su Virus Text Files.
Irin wadannan nau’ukan kwayoyin cuta idan
suka shigi kwamfuta ba a ganin su kai tsaye,
don lungu suke samu su buya, iya kwatancin
umarnin da ke cikin su, daga marubuci ko
makirkirin su. Sai nau’i na biyu da ke zuwa a
matsayin masarrafa. Watau jakar bayanai da za
a iya shigar ma kwamfuta, a iya budo shi ana
amfani da shi. Su kuma ana kiransu Virus
Executable Files. Idan har ka matsa su don
shigar ma kwamfuta, to ka nemo mata rigima.
Hanya ta uku ita ce ta jakunkunan bayanan da
ke dauke da hotuna masu irin wadannan
kwayoyin cuta. Galibi hotuna ne masu dauke da
tallace-tallace; na batsa ko kuma na harkan
caca. Watakila mai karatu yayi ta mamaki: yaya
daga shigar da jakan bayanai a cikin kwamfuta
kuma sai ta rikice ko sume? Ai ba a nan take ba,
wai an danne bodari a ka. Idan kana son gane
yadda lamarin yake, ka kwatanta da jikin dan
Adam. Idan kwayar cuta ta shiga jikin sa, to dole
ne sai an samu sauyin yanayin lafiya a tattare
da shi. Don me? Saboda kwayar cutar ta sha
banban da dabi’ar jikin sa. To haka ma irin
wadannan bayanai da ke shiga kwamfuta;
umarni ne a cikin su da maginin su ke baiwa
kwamfutar, kuma a matsayinsa na wanda ya san
yadda gini ko zubin tsarin manhajan ta yake, ya
san hanyoyin da zasu iya zama matsala a
gareta. Don haka da zaran sun shigo, sai ta
rikice.
Hanyoyin Kamuwa da Yaduwa
Wadannan cututtuka sun fara samuwa ne tun
kirkiran kwamfuta da manhajojin ta, kuma akwai
manyan hanyoyi guda biyu da kwamfuta ke iya
kamuwa da su. Hanyar farko ita ce ta amfani da
hanyoyin shigarwa ko fitar da bayanai ta
kwamfuta, watau Storage Devices, a Turance.
Ma’adanai ne da ake amfani da su wajen shigar
ma kwamfuta bayanai na haruffa da taswiro ko
hotuna da dai sauran su. Sun hada da Floppy
Disk, mai cin mizani miliyan daya da rabi, da
kuma Zip Diskette, mai cin mizanin bayanai
sama da miliyan goma, da kuma Flash Disk,
wanda a yanzu aka fi amfani dashi. Shi Flash
Disk dabaka-dabaka ne; akwai mai cin miliyan
dari da ashirin da takwas, da mai cin miliyan
dari biyar da goma sha biyu, da kuma mai cin
biliyan daya har dai zuwa sama. Dukkan
wadannan ma’adanai ne da ake amfani da su
wajen shigar da bayanai ko debo su daga
kwamfuta. Idan suna dauke da kwayoyin cutar
kwamfuta, ka shigar dasu cikin kwamfutarka, to
nan take zasu nemi wuri a cikin ta su labe.
Hanya ta biyu ita ce ta hanyar Intanet. Nan ma
kana iya jefa kwamfutarka cikin hadari. Idan ka
sauko (Download) ma kwamfutarka da
masarrafa (Software) mai dauke da kwayoyin
cuta, yanzu zata kamu. Haka idan ka cika
ziyartan gidajen yanar sadarwa na caca da
batsa, kana matsa duk hoton da ka gani, kana
iya kamuwa da wadannan cututtuka. Haka kuma
idan ka cika sauko (Download) da duk jakar
bayanai da ka ga an aiko maka ta Imel dinka, ba
tare da ka san mai aikowa ba, nan ma kana iya
kamuwa da wannan cuta. Galibin sakonnin da
ake aiko mana cikin Imel din mu wadanda bamu
san mai aiko su ba, watau Spam Mails, duk za
ka samu suna dauke da makalutun bayanai
(Attachments), kuma sau tari za ka samu akwai
kwayar cutar kwamfuta cikin su. Wadannan, a
takaice, su ne shahararrun hanyoyin da ake bi a
kamu da cutar kwamfuta.
Alamun Kamuwa
Idan kwamfuta ta kamu da cuta, ba kowa ke iya
ganewa ba, sai wanda ya saba mu’amala da ita
a kullum. Ko shi ma, ba kowanne zai iya ganewa
ba. Kwamfuta na iya kamuwa da cuta, amma
kuma ba a gane ba. Kai a takaice dai, akwai
alamun da za a iya ganewa ba tare da sai an
sha wahala ba. Akwai kuma wadanda sai
kwararre ke iya gane su. Nau’ukan farko sun
shafi shahararrun alamu masu bayyana,
wadanda ko da baka san cewa kamuwa tayi ba,
ka san cewa akwai matsala. Sun hada da yawan
saibi. Idan ka bata umarni, sai ta dauki lokaci
kafin ta karbi umarnin ka. Muddin kaga haka
yaci gaba, lokaci mai tsawo, to akwai matsala.
Haka idan kaga tana yawan sumewa da kamewa
alhalin kana aiki da ita. Wannan shi ake kira
Hanging a turancin kwamfuta. Muddin ta ci gaba
da haka, kuma ba a jone kake da Intanet ba, to
akwai matsala. Haka idan ka nemi wasu
jakunkunan bayanan ka ka rasa, ko kuma ka
samu wasu, ka rasa wasu, ko kuma ka budo
jakunkunan, ka samu wasu bakin bayanai da
baka san dasu ba, masu dauke da wasu irin
sunaye marasa kan gado, to da matsala. Haka
idan ka kasa bude jakunkunan bayanan ka gaba
daya, ko kuma idan ka budo guda daya, sai su yi
da budowa ba tare da ka budo su da kanka ba,
to duk alama ne da ke nuna cewa kwamfutar ka
ta kamu. A wasu lokuta kuma zaka samu
kwamfuta na mutuwa da kunna kanta, ba tare ka
kashe ta ba, haka kawai! Duk wannan alama ne
da ke nuna kamuwa. Idan kuma cutan ya ga
dama, yana iya gurbata maka bayanan ka gaba
daya; duk wanda ka budo sai dai ka yi ta ganin
wasu shirmen sunaye ko haruffa. Duk aikin su
ne. A wasu lokuta kuma kwamfutar na iya
kamuwa, amma ba za ka taba sani ba. Galibin
lokuta sai an sanya manhajar goge cutar
kwamfuta, watau Antivirus Software, sannan ake
iya ganowa da cire su. Idan kuma cutar mai
tsanani ce, illolin ta na iya haddasa ma
kwamfuta hadari mai girma, ta yadda sai an
sanya mata wani sabon ruhi ko babban manhaja
sannan za ta iya ci gaba da aiki. Wannan
manhajan ba ya iya magance mata matsalolin
ta.
Nau’ukan Kwayoyin Cutar Kwamfuta
Suna nan da yawa! Da farko dai shahararren
sunan da aka fi sanin su dashi shine Computer
Virus, a turance. Amma a karkashin wannan
suna akwai rukuni wajen hudu, iya gwargwadon
girma/tsanani ko kuma yanayin illa ko aikin da
cutar ke iya yi a cikin kwamfuta. Da farko akwai
kwayoyin cututtukan da ake tsofa su cikin
masarrafan kwamfuta da galibi ake samu kyauta
a Intanet. Su ana kiran su Spyware, kuma aikin
su shine yin leken asiri ga uban gidan su, watau
wanda ya gina manhajan kenan. Akan sanya su
ne cikin masarrafan, don duk lokacin da ka jona
kwamfutar ka da Intanet, wannan masarrafa da
ka samo kake amfani da ita kyauta, ta rinka aika
ma mai shi da bayanai kan tsarin abinda kake yi.
Yai haka ne don wata manufa mummuna ko
kyakkyawa. Galibi na yin haka ne don sanin
yawan wadanda suke amfani da wannan
manhaja nasu. Amma a ka’ida bai dace ba. Sai
kuma rukuni na biyu, watau Malware, wadanda
su ma a cikin manhajojin kwamfuta da ake samu
ta Intanet ake sanya su. Sai dai sabanin na
farko, su wadannan aikin su na cutarwa ne kai
tsaye. Idan ka sake suka shiga kwamfutarka,
nan da nan za ka fara ganin alamun rashin lafiya
tattare da ita. A kataice dai cuta ce ta kwamfuta
mai halakarwa. Sai rukuni na uku, wadanda ake
kira Adware. Su kuma galibi idan kana yawan
mu’amala hotunan tallace-tallace ne zaka iya
kamuwa da su. Cututtuka ne na kwamfuta, masu
dauke cikin hotuna masu motsi ko marasa
motsi. Idan ka matsa (Click) hotunan da suke
dauke dasu, da zaran shafin hoton ya budo, to
kwamfutarka ta shiga kenan, muddin ka ci gaba
da ta’ammali da wannan shafi. Wadannan
cutattuka an fi samun su a gidajen yanar
sadarwa na caca da batsa da kuma katuttukan
gaishe-gaishe (Greetings Cards). Sai rukuni na
karshe, watau Trojan Horse. Idan irin wannan
cuta ya shiga kwamfutarka, to gaskiya hanya
mafi sauki shine kayi mata juyen ruhi kawai,
watau Formatting. Domin yana mallake ta ne
gaba daya, ya bi ta ya mamaye; ya hana ka aiki
da komai a kwamfutar gaba daya. Idan Trojan
Horse ya auri kwamfutarka, sai makabarta,
Yalla! Domin zai mallake manyan ma’adanta ne,
watau Disk Drives, ya hana ka budo komai, ya
rikita kwamfutar gaba daya. Wasu lokuta idan ya
ga dama, sai ya dasa wani shafi guda daya,
wanda zai rufe fuskar kwamfutar ma gaba daya;
baka iya komai. Idan kwamfutar ka a jone take
da Intanet, ya fuskanci kana niyyar budowa ko
kuma sauko da manhajar goge cutar kwamfuta,
sai ya kashe kwamfutar gaba daya, ya sake
kunna maka ita. Amma idan ba can ka nufa ba,
shikenan. A takaice dai, cuta ne mai lura da
dukkan abinda kake yi. Idan aikin ka ya shafi
jakunkunan bayanai ne zalla, sai ya barka (iya
gwargwadon umarnin da uban gidan sa ya
bashi). Amma idan ya ga ka nufi Intanet da
rariyar lilo da tsallake-tsallaken ka, watau
Browser, sai ya kashe kwamfutar kawai. Wannan
ya taba faruwa da ni shekaru kusan uku da suka
gabata. Sai da na sauya ma kwamfutar wani
sabon ruhi na zauna lafiya.
Kammalawa
A bayyane yake cewa babban matsalar da ke
damun kwamfutoci a halin yanzu shine
cututtukan da ke mata illa wajen hana ta aiwatar
da ayyukan ta cikin sauki.
please Share And Comment.
No comments:
Post a Comment
Comment