Leave a message

Breaking

Post Top Ad

| Latest News | Entertainment | Seince & Technology |Advertisement |Videos| Books | Love Quate & Others |

Wednesday, 13 May 2020

[JARIDAR LABARAI] Shira Ta Musamman Da Najib NB Srk Akan Harkar Fasahar Zamani.



RAYUWAR MATASA

Barkan mu da sake saduwa acikin sabon shirin mu na "BAJAKOLIN RAYUWA MATASA" wanda yake kawo mu Tarihin Rayuwar matasa da kuma irin gwagwarmayar su da nasarorin su da kalubalen su na rayuwa. Wanda yake zuwar muku a duk larabar Mako da misalin 11:00am.

Ni Sani idris Tudun wada da nasaba gabatar muku, Yau muna tare da babban bakon mu matashi masani akan harkar na'ura mai kwakwalwa #NAJIB NB srk a fannin yanar gizo wato (Networking).

Sani Idris:
NAJIB NB SRK muna maka barka da zuwa.

Najib NB Srk:
Yauwa Barka Dai, Ina Godiya Da Wannan Gayyata Da Akaimin Zuwa Wannan Shafin Mai Albarka.
Sani Idris:
Masu karatu za su so suji wanda suke tare dashi ?

Najib NB Srk:
To Da Farko Suna Na Nagaskiya Shine; Najib Muhammad Ya'u, Amma Amfi Sani Na Da "Najib NB Srk".
Sani Idris:
Ko zaka iya bawa mai karatu takaitaccen tarihin ka?

Najib NB Srk:
Okay! To Nidai Anhaife Ni A Garin Kano A Cikin Karamar Hukumar (Gwale L.G.A), Gidan Mu Gidan Sarauta Ne Don Kaka Na Mai Suna Ya'u Shine Shugaba A Yankin Mu Na Unguwar "Ja'en Yamma A" .Baya Da Haka Nayi Karatuna Tun Daga Matakin "Pri-Nusery" Har Zuwa "Secondary" A Wata Makaranta Wacce Take Unguwar Mu "JA'EN" Mai Suna *Waya School Complex*.Inda A Yanzu Ina Shirin Ci Gaba Da Karatuna Don Nashiga Makarantar Gaba Da Secondary Wato "Jami'a Ko Kwaleji".Sannan Kuma Nayi Karatun Addini Dede Bakin Gwargwado. Wannan Shine Takaitaccen Tarihi Na A Takaice.
Sani Idris:
To kace yanzu kake burin shiga makarantar gaba da sakandire to kana da wani abu da kake da burin ka karanta ne?

Najib NB Srk:
Eh! Tabbas Ina Da Burin Karantar Aikin Jarida, Amma Sakamakon Yaya Na (Hassan Mamuda Ya'u) Aikin Yake A Gidan Radio (Dala Fm Kano) Sai Na Chanja Zuwa Karantar "Computer Science" Wato Ilimin Fasahar Na'ura Mai Kwakwalwa.Inda A Yanzu Duk Da Ban Fara Karantar Fannin Ba, Amma Ina Da Sani Kan "Computer" Da Duk Wasu Al'amura Da Suka Shafi *Networking* Nakan Kirkire Su Ko Na Hadawa Mutane A Biya, Harma Na Maida Hakan Sana'a.
Sani Idris:
A ina kasamo shi wannan sunan da akafi sanin ka dashi "Najibkhan"?

Najib NB Srk:
Uhhm! Wannan Suna Nafara Amfani Da Shine A Shekarar 2016 Sakamakon Son Indiya Da Nake Yi, Inda A Yanzu Inajin Yaren Indiyanci Sama-Sama.Amma, A Yanzu Na Cire Kalmar *Khan* Daga Jikin Suna Na Sakamakon Wasu Dalilai, Duk Da Hakan Babu Illatarwa Don Nasa Kamlar Jikin Suna Na.
Sani Idris:
Ita dai kalmar "khan" kalmar indiyanci ce kenan, ko menene ma'anarta?

Najib NB Srk:
Tabbas! Kalmar *Khan* Kalma Ce Da Duk Wani Musulmi Ko Dangin Musulman Indiya Ke Amfani Da Ita.Wato Ita Kalmar Kamar Wani Linzami Ne Wanda Yake Fassarawa Indiyawa Cewa Duk Wanda Kalmar Khan Ta Zamto A Karshen Sunan Sa, To Musulmi Ne. Wannan Dalilin Ne Yasa A Matsayina Na Musulmi Kuma Wanda Yake Sha'awar Fina-Finan Indiyawa Da Kuma Sudin Tasa Nima Na Rikida Na Koma *Khan*
Sani Idris:
Naji abaya kace gidan ku gidan sarauta ne wacce sarauta kenan?

Najib NB Srk:
Eh! Kamar Yanda Na Gaya Ma Kaka Na Shine Ke Rike Da Jagorancin Unguwar Mu, Kamar Ace (Mai Gari, Dagaci, Hakimi, Mai Unguwa).To Shi Yana Rike Da Sarautar "Mai Unguwa".
Sani Idris:
Kenan kaima kayi gadon sarauta wataran zaka iya zama sarki kenan?

Najib NB Srk:
Abun Na Allah Ne, Domin Idan Allah Ya Rubuta Alkalamin Kaddara Ta Kan Zama Sarki, To Babu Abinda Zai Hana.
Sani Idris:
Bayan sana'ar Networking akwai wata sana'ar da kakeyi ne?

Najib NB Srk:
Eh! Amma Gaskiya Wannan Itace Babbar Sana'ar Da Nake Alfahari Da Ita, Don Nasamu Alkairai Sosai Da Ita Kam.Bayan Nan Ina Sana'ar Saida "Plawood" Wato Kato Irin Na Hada Gado Ko Sif Da Sauran Su.
Sani Idris:
"Najib NB Srk" nima na ďa na sakamakon chanjin da kasamu na burin da kake dashi na karatun jarida kuma yanzu bashi bane idan ka tuna kana jin wani abune a ranka?

Najib NB Srk:
Gaskiya Banji Wani Chanji Ba Duba Da Tun Barko Mafarkina Da Kuma Ra'ayina Yafi Karkata Akan Fanni Kimiyya Da Fasaha.Don Ban Manta Lokacin Da Nake Shafe Kwanaki Da Tsahon Lokaci Ina Bincike Da Nazari Cikin Dare Da Waya Ta, Kan Abubuwan Da Suka Shafi Kirkirar Shafin Yanar Gizo Da Kawata Shi Wato (Web Design).Nasha Kwana Akan Wadannan Al'amari Tun Anama Fada A Gida Saboda Yanda Nake Shafe Rabin Lokacin Rayuwata Kan Waya Android Kafin A Fahimci Irin Abinda Nake Da Ita Da Kuma Muhimmancin Sa.A Yanzu Alhamdulillah Nasami Abinda Nake Kan Kwarewa Akan Fannin (Blogging) Da Kuma Hada Manhaja Wato (Android Application).Kuma A Yanzu Na Koyar Da Wasu Wannan Harkar Musamman Koyar Da (Blogging) Da Kuma Zubin Fasahar Yaren "HTML, CSS, JAVA.Baya Da Wannan Sana'a Ta Networking Ina Yin Design Na Hada Hotuna Da Kawata Su, Kuma Dukkan Su Nakoyi Wadan Nan Abubuwa Ne Da Waya Ta.Saboda Banda Arzikin Siyan Computer A Lokacin Baya.
Sani Idris:
A lokacin da kake ta kokarin kaga ka kware a wannan bangaran na Networking wanne irin kallo mutane suke maka musamman abokan ka?

Najib NB Srk:
Harka Tunan Baya! Eh Gaskiya A Unguwar Mu Saida Aka Samin Ido, Don Yanda Bana Jure Mintuna 10 Batare Dana Danna Waya Ta Ba Inde Da Chaji.Saboda Sabo Danayi Inde Aka Ganni A Guri Ni Kadai To Za'a Ganni Nakasance Da Karamar Mata Wato Waya Ina Danna Ta, Kuma Har Yau Har Gobe Bancika Saka Wayata A Aljihu Ba Saboda Sabon Riketa A Hannu Na.Don Ina Da Tabbaci Ko Unguwar Mu Kazo Kace Waye Ko Ina Zaije Yana Rike Da Wayar Sa A Hannu Za'ace Ma *Najib* Ne . To Haka Tasa Wasu Ke Cemin Mayen Waya, Don Ban Manta Wani Abokina Da Yake Cemin Mai Idon "Screen" Wato Da Anganni Anga Wanda Yafi Dora Idon Sa Kan Sikirin.Amma Duk Da Abin Da Su Ke Baya Damuna Saboda. (Baiyana Fa'ida Kan Allon Jigon Tushe, Shike Dabbaka Rubutun Ka'idar Abinda Kake Son Cimmawa A Rayuwa), Sannan (Duk Halittar Dake Irga Salon Ka, To Tabbas Bazata Taba Kirkirar Nata Salon Ba) Ma'ana: "Duk Wanda Yake Sama Ido Kan Lamarin Ka, To Sam Bazai Iya Cimma Nasa Lamarin Ba). Ni Kuma Nayi Imani Da Sanya Tubalin Abu Kyakkyawa Mai Amfani Akan Kudiri Na, Hakan Tasa Ban Damuwa Da Haushin Nakasasshen Kare Wato MAHASSADI KO DAN SA IDO KAN HURUMIN DA BA RUWAN SA. Wannan Shine Abokina.
Sani Idris:
Idan kasamu gurbin karatu ya zakayi da sana'ar ta ka wacce zaka zaba daga ciki Networking ko plawood ?

Najib NB Srk:
Eh! Gaskiya Zan Iya Jingine Ta Saida "Plawood" Don Dama Tuni Nama Bata Baya.Amma Harkar Networking Banjin Zan Iya Rabuwa Da Ita Gaskiya, Don Koda Ma Na Karanci Computer To Shima Babin Yana Da Babbar Alaka Da Networking.A Zahirin Gaskiya Sana'ar Networking Da Design Na Hotuna Banji Zan Iya Rabuwa Da Su, Don Fannika Ne Wayanda Nasha Bala'in Wuya Kan Na Iya Su.
Sani Idris:
Me kake kallo a matsayin nasarar da kasamu a rayuwa?

Najib NB Srk:
To Gaskiya Babbar Nasarar Dana Samu Kan Wannan Harka Shine; Na Farko Na Samu Kudi, Na Dinka Sutturu, Na Biya Bukatuna, Gashi Kuma Na Koyawa Wasu Harkar Kuma Alhamdulillah Zun Iya.Bayan Nan Ina Da Shafi Wanda Yake Yawan Maziyarta Sama Da 100,000+, Ina Zaune Kanji Mutane Nakirana Daga Sassan Jahohi Na Najeriya Da Kuma Sakonnin Fatan Alkairi Ta Asusu Na Na Email Harma Da Yan Kasar Waje.Bayan Nan Abinda Nake Jin Dadi Da Shi Shine; A Yanzu Idan Akai Searching Din Suna Na (Najib NB Srk) A Google SEO Za'a Iski Bayanai Da Shafina Harma Da Wasu Accounts Wayanda Suke Da Alaka Dani. Abu Nagaba Dazan Daga Nace Nasara Ce Shine: Na Kirkiri Manhaja Wato Application Na Android Na Karatu. Apps Din Sune Kamar Haka;
• Mukoyi Computer
• Mukoyi Blogger
• Mukoyi HTML
• Mukoyi CSS
Dukka Bayanai Ne Danayi Cikin Harshen Hausa Inda Al'ummar Mu Zasu Koyi Komai A Saukake Na Game Da Fasahar Zamani.
Sani Idris:
To kai gashi Makaranta zaka tafi kaga ba maganar aure kenan, amma ba mu sani ba ko kana soyayya?

Najib NB Srk:
Ikon Allah ! To Gaskia A Baya Nayi Soyayya Wacce Take Ta Gaske, Kuma Daga Baya Aka Yaudari Zuciya Ta.Wato Wacce Nake So Sai Naji Tacemin Ai Aure Za'ai Mata Anbata Wani.Nayi Bakin Ciki Sosai Duk Da A Lokacin Koda Zancen Soyayya Nakai Gida Fada Za'aimin. Tun Daga Lokacin Nadena Zurfafawa A Soyayya, Don Bazance Nadena.Domin Dalilin Dayasa Bana Zurfafawa Nasan Yanzu Matakin Aure Na Ko Kuma Lokacina Na Sha'awar Sa Baizo Ba, Hakan Tasa Inde Nayi Budurwa Ko Wata Ta Nuna Tanaso Na, To Ina Fada Mata Gaskiya Ba Aure Zan Ba.Uhhm Sai Dai Kasan Ba'a Rasa Soyayyar Nan Ta Wasa Ko Ta Rage Lokaci, Zan Iya Cewa Ita Nake.Don A Yanzu Banda Tsayayyiyar Masoyiya☺️.
Sani Idris:
A kafafen sadarwa na zamani wacce kafison ta, ammali da ita kuma mai yasa kafinta?

Najib NB Srk:
Gaskiya Nafison Kafar Sada Zumunta Na *Facebook* Domin Muhalli Ne Wanda Ya Hada Kowacce Iriyar Al'umma, Sannan Shine Dandali Gagara Misaltawa A Duniya.Saboda Zaka Iya Samun Wanda Baya Twitter Yana Facebook, Ko Wanda Baya Whatsapp Sai Facebook, Ko Kuma Duka Biyun Wato Yana Whatsapp Da Twitter Harma Da Facebook Din.Sannan Shafin Facebook Yanda Suka Saukaka Inda Ko Baka Da Data Zaka Iya Amfani Da Shi, Sai Kuma Sauki Da Yake Dauke Da Shi Na Sarrafawa Mutum Ko Be Iya Karatun Hausa Ba Yakan Bude Yaga Hotuna Ko Bidiyo Ta Ciki.Abaya Nafison Kafar Sada Zumunta Ta *2go*, Amma Yanzu Shafin Facebook Gaba Yake Da Kowanne Shafi A Wajena.
Sani Idris:
Wanne abune ke burge ka/ faranta maka rai ?

Najib NB Srk:
Gaskiya Abinda Yafi Farantamin Rai Na Farko Itace Mahaifiya Ta, Don Aduk Sanda Nashiga Damuwa Idan Natuna Da Nasihar Ta A Gareni Kan Hakuri Da Lamarin Rayuwa Sai Naji Dadi.Sai Kuma Yanayin Da Ake Ruwan Sama, Da Kuma Karatu Da Soyayya.Suna Cikin Abubuwan Da Sukafi Kawatar Da Zuciyata.
Sani Idris:
Tsakanin yanayin zafi da sanyi wanne kafiso?

Najib NB Srk:
Gaskiya Nafison Yanayin Zafi Saboda Jikina Yakan Jure Zafi, Sannan Fatar Jikina Tafi Kyau Sannan Kuma Banfiye Cin Abinci Da Yawa Ba Inde Zan Dinga Shan Ruwa Akai-Akai.Lokacin Sanyi Kuma Gaskia Ko Bacci Banfiye Yi Ba Da Daddare Hakan Yasa Nafiyin Project Dina Da Sanyi Saboda Nafi Jin Dadin Aikina Na Cikin Dare Wanda Ya Shafi Networking, Sannan Nafi Cin Abinci Sosai Ga Kuma Yanayi Na Yafi Chanjawa A Lokacin Saboda Sanyi Yanda Kowa Yake Komawa A Lokacin.
Sani Idris:
To saboda halin lokaci wanne irin kira zakayi ga yan uwanka matasa?

Najib NB Srk:
Masha Allah! Kiran Da Zanyi Shine: Mudagewa Cimma Kyawawan Kudiran Mu, Sannan Kada Mu Dogara Da Damar Wani.Wato Damar Da Muke Da Ita Itace Yancin Mu Ba Ta Wani Ba.Baya Da Haka Akoda Yaushe Mu Dabbaka Sinadarin Dagiya A Zuciyar Mu Inde Muna Son Cimma Nasara.Saboda Rayuwa Fasaki Shike Tabbatar Da Martabar Ta, Inde Ka Gina Tushen Aikin Ka Kan Aiki Tukuru, Hakuri, Kishin Kai, Da Jajurcewa.To Lallai Za Ka Sami Abinda Kake Son Cimma Komai Wuyar Sa.Don Ban Manta Cewa (Duk Wanda Ya Sha Wahalar Shuka Bushiya, To A Kwana A Tashi Zata Baka Inuwa Ko Iska), Ma'ana: Inde Kai Aki Tukuru, To Lallai Gaba Zakaji Dadi. Wannan Itace Shawarata A Takaice Ga Matasa.
Sani Idris:
Da ace matasa kowa zai kama sana'a da wanne irin cigaba kake ganin za'a samu?

Najib NB Srk:
Gaskiya Za'a Samu Ci Gaba Da Kuma Rage Zaman Banza Ga Sauran Al'umma, Domin Arzikin Kasa Shine Sana'a, Kuma Kowacce Kasa Martabar Ta Bata Tabbata Dede Sai Da Sana'a Ga Yan Kasar.Sannan Kirana Ga Masu Dama Shine Idan Kana Da Damar Daukan Mutun Uku Koma Daya Ne Aiki Muyi Kokarin Daukan Sa Aiki, Don Sanya Masa Rigar Mutunci.Nasha Gwagwarmaya Kan Kan Neman Aikin Rufin Asiri A Baya Kafin Nafara Sana'ar Networking. Hakan Tasa Nake Tausayin Matasan Da Basa Da Sana'a Duk Da Wasu Girman Kaine Ke Hanasu Yin Sana'a.Allah Dai Ya Taimaka Mana Ameen.
Sani Idris:
Anan zamu dasa aya a wannan muhimmiyar tattaunawa tamu da kai, sai dai wanne irin fata zaka yiwa wannan shafi na JARIDAR LABARAI?

Najib NB Srk:
Alhamdulillah! To A Karshe Fatana Ga Wannan Shafi Shine Allah Yakara Dabbaka Shi Zuwa Matakin Nasara Mayalwaciya Tare Da Dukkan Ma'aikatan JARIDAR LABARAI. Sai Shawarata Ga Wannan Shafi Dama Jagororin Sa Shine: Sai Anci Gaba Da Hakuri Da Abinda Al'umma Zasu Ce Da Kuma Jajurcewa.Sannan Kuma Yana Da Kyau Ku Samarwa Shafin Dandalin Yanar Gizo Inda Duniya Zata Dinga Kallon Labaran Ku Da Karanta Shi Kamar Yanda BBC Suke.Don Sular Hauhawar Shafin Shine Yanda Suka Samarwa Shafikan Su Dandali Da Kuma Taskar Akwatin TV Yanda Za'a Dinga Ganin Labaran Su Kai Tsaye. Wannan Shine A Takaice.
Sani Idris:
Mun gode da bamu aron lokacin ka Allah ya saka da Alkhairi musha ruwa lafiya

Najib NB Srk:
Ameen Nagode Sosai, Mu Huta Lafiya.

Domin neman karin bayani:

CLICK HERE • Sani idris Tudun wada
• CEO:Jaridar Labarai
• 08030610691.

WEBMASTER

Ina Masu Bukatar Da A Bude Musu Shafin Yanar Gizo Ko Kawata Musu Shi?.Kai Tsaye Idan Ana Bukata Za'a Iya Samun NAJIB NB SRK Ta Nambar Sa Kamar Haka: 08168211346, Mungode.

No comments:

Post a Comment

Comment

Post Top Ad

Your Ad Spot
+widget
a