YANCIN KAI.............................
.
A ranar 15 ga watan Agusta ne kasar Indiya
ta
ke bikin murnar samun 'yanci kai daga
turawan
na Ingila, mulkin mallakar da ya zo karshe a
shekarar 1947.
.
Indiya dai ta samu 'yancin kai bayan fadi-
tashin da
wasu 'yan gwagwarmaya suka shafe tsawon
lokaci
suna yi.
.
Mutane irinsu Gopal Krishna Gokhale, su ne
suka
fara kaddamar da kiraye-kiraye ga al'ummar
kasar
da su fito su bayyana bukatarsu ta samun
'yancin
kai, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da
dukiyoyi.
.
A duk rana irin ta yau firai ministan da ke kan
mulki
na daga tutar kasar tare da yin jawabi ga
miliyoyin
Indiyawa, hakan wata al'ada ce da kasar ta
gada
daga wajen firai ministan farko, Jawaharlal
Nehru.
.
Gwagwarmaya
.
A shekarar 1929, jam'iyyar National Congress
ta
ayyana ranar 26 ga watan Janairu a matsayin
ranar
samun 'yancin kasa, sai dai ta rika yin taruka
a
boye saboda gudun fushin Ingila.
.
Haka aka rika tafiya har zuwa lokacin da
Mohandas
Karamchand Ghandi, ya dawo kasar
sakamakon
kiransa da manyan 'yan siyasar kasar suka yi
na ya
zo domin ya taimaka musu a kawo karshen
mulkin
mallaka.
.
Zuwan Mahatma Ghandhi ne ya sauya tafiyar
siyasar kasar, kasancewarsa mutum mai
tsananin
son zaman lafiya da daidaito ta fuskar
zamantakewa, ya shiga gaba don tabbatar da
cewa
turawa sun daina matsawa Indiyawa ta fuskar
haraji da bautar da su da sauran su.
.
Sai dai yunkurin da 'yan jam'iyyar National
Congress suka fara na ganin Indiya ta samu
'yanci,
ya samu tsaiko a lokacin da yanki Pakistan
mai
rinjayen Musulmai ta ki amincewa da zama
karkashin Indiya, ta kuma yi yunkurin ballewa
kwata-kwata.
.
Yunkurin Pakistan ne ya raba hankulan
turawa,
suka rasa ta inda zasu fara, saboda haka aka
jibge
sojoji a tsakanin Pakistan da Indiya domin
ganin an
dakile 'yan fafutukar, lamarin da ya kai ga
mutuwar
mutane miliyan daya.
.
Daga bisani turawa sun ayyana Pakistan a
matsayin
'yantacciyar kasa a ranar 14 ga watan Agusta,
1947, watau ta girmi Indiya da kwana daya
wajen
samun 'yanci.
.
Duk da alkawura da Gwamnan Indiya Clement
Attlee ya yi, na cewar za a bai wa kasar 'yanci
a
watan Yunin 1948, manyan 'yan siyasa sun ki
amincewa da bukatarsa, inda a daren ranar
15 da
misalin karfe 11 na dare, suka hadu domin
bayyana matsayarsu kan gwagwarmayar da
ake ta yi ta samun 'yanci.
.
Cikin wadanda suka halarci zaman akwai
shugaban kasa Rajendra Prasad, da wasu
manyan
kungiyoyi na mata.
.
Gaba daya mahalarta taron sun mika kansu
don
ganin an fitar da kasar daga kangin talauci,
fatara
da kuma bauta.
.
Firai minista Jawaharlal Nehru, ya yi jawabi
mai
ratsa zuciya a taron, inda ya rika karfafa
gwiwa kan
muhimmanci tashi domin a kwaci 'yancin kai.
.
Haka kuwa aka yi, washegari dole turawa suka
ayyana Indiya a matsayin 'yantacciyar kasa
don
kaucewa asarar rayukan da aka kwashe
watanni
ana yi.
.
Amma duk da haka kasar ba ta fara aiki da
kundin
tsari na kashin kai ba sai a ranar 26 ga
watan
Janairun 1950.
.
Shugabannin farko
.
Bayan samun 'yancin ne, al'umma kasar suka
rika
kiran sunan Mahatma Ghandi da jinjina masa
sakamakon irin gudunmuwar da ya bayar a
nasarar da aka samu.
.
Wasu na bayyana sunansa a matsayin sabon
shugaba, sai dai a nasa bangaren, ya nuna
sam bai
sha'awar mulki, sai ma kira da ya yi ga
al'ummar
kasar mabiya addinin Musulunci, mabiya
addinin
Hindu da mabiya addinin Sikh da su yi hakuri,
su
zauna lafiya da juna.
.
Daga bisani aka nada Jawaharlal Nehru firai
minista, sai kuma Lord Mountbatten a
matsayin
Gwamna (kafin kudin tsarin mulkin kasar ya
fara
aiki).
.
A bangaren Pakistan kuma aka rantsar da
Muhammad Ali Jinnah a matsayin Gwamna.
.
Tattalin arziki
.
Tattalin arzikin India a kullum yana habaka
ne ta
hanyar kimiyya da fasaha da likitanci da
kuma
harkar fina-finai.
.
Bangarorin kimiyya da kiwon lafiya kawai na
bayar
da kaso 35 cikin dari ga tattalin arzikin kasar.
.
Kasar ta Indiya na kwararrun likitoci wadanda
ke
aiki asibitoci daban-daban na duniya, yayin
da
kasar ke da asibitoci da kayan aiki na zamani,
lamarin da yasa dumbin mutane, musamman
daga
kasashe masu tasowa ke zuwa kasar domin
neman
magani.
.
Har ila yau kasar ta yi fice wajen samar da
magunguna a duniya.
.
Wannan bangaren ma yana taimakawa kasar
wajen bunkasa tattalin arzikinta.
.
A bangaren kere-kere kuwa, India tana kera
ababen hawa kamar su Jirgin sama da motoci
da
babura da kuma kekuna.
.
Kuma ana fitar da irin wadannan kayayyaki
zuwa
kasashen ketare, wanda a bangaren na kere-
kere
kawai India na samun kaso 45 cikin dari na
kudaden shigarta. Sai kuma bangaren fina-
finai
wato na Bollywood.
.
Bollywood
.
Bayan harkar fina-finai ta Amurka, wato
Hollywood, Bollywood shi ne na biyu a duniya.
.
Fina-Finan Bollywood na taka muhimmiyar
rawa
wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, domin
yana
bayar da kaso 5.1 cikin dari ga tattalin
arzikin
kasar,baya ga samar da ayyukan yi ga
dumbin
matasa.
.
A duk shekara masana'antar Bollywood tana
samar da kudin shiga akalla dala biliyan
takwas, ko
fiye da haka ga Indiya.
.
Baki daya Indiya na samun kudaden shiga
kusan
dala tiriliyan biyu daga wadannan hanyoyi
uku...
No comments:
Post a Comment
Comment