TAJ-MAHALTaj-Mahal:•Yana Daya Daga Cikin Abubuwan Al’ajabi Bakwai 7 Da Ake Da Su Yanzu Haka A Duniya. Wannan Gini Na "Taj Mahal" Tarihi Ya Bayyana Cewa Wani Kabari Ne Da Sarki (Shah-Jahan).Ya Sa Aka Ginawa Matarsa Ta Uku Mai Suna "Mumtaz- Mahal". Domin Tunawa Da Ita A Matsayinta Na Wacce Yafi So Da Kauna A Rayuwarsa. Wannan Kasaitaccen Gini Na "Taj Mahal" Yana Yankin (Agra) Dake Kasar (Indiya), Kuma Anbayyana Cewa Shi Ne Kyautar Soyayya Mafi Tsada A Duniya. Ginin yana da Tsawon Mita 73 (Dai-dai da kafa 240) "Ustaz Ahmad Lahauri". Shine Yazana Taswirar Ginin. Sarauniya "Mumtaz Mahal" Ta Rasa Ranta Ne Lokacin Da Ta Zo Haihuwa Ta 14. Mutuwarta ta Girgiza Sarki "Shah Jahan" Matukar Girgizawa Inda Ya Sha Alwashin Yi Mata Kyautar Da Za A Rika Tunawa Da Ita Har Duniya Ta Tashi. Haka kuwa Aka Yi.Sarki "Shah Jahan ".Ya Tura Sassa Daban- Daban Na Duniya Aka Nemo Masa Kwararrrun Magina Sama Da Dubu 20 Suka Kama Aiki Dare Da Rana Domin Wannan Gini Na "Taj Mahal". An Fara Ginin Ne A Shekarar 1632 Aka Kammala A Shekarar 1653, Kimanin Shekara 22 Aka Shafe ke Nan Ana Gina Wajen. A Wancan Lokacin Ginin Ya Ci Kimanin RufiS Indiya Har Milyan 32, Wanda Darajarsu a Yanzu Sun Kai Rufi Biliyan 52.8, (Daidai Da Dalar Amurka Miliyan 827).Bayan an Kammala Ginin A Shekarar 1653, Sai Sarki "Shah-Jahan". Ya Sa Aka Tara Kwararrun Maginan Da Suka Yi Aikin Tare Da Ba Da Umarnin Datse Hannayensu. Dalilansa na Wannan Danyen Aiki,Shi Ne Don Kada Su Je Su Sake Gina Wani Makamancinsa A Wani Wuri. A yau An Wayi Gari Ginin Taj Mahal.Mai Shekara 383,Shi Ne Gini Guda Daya Da Babu Makamancinsa A Duk Fadin Duniya Wajen Tsari da Daukar Hankali.A halin yanzu Gawar "Shah Jahan" Da na Matarsa "Mumtaz Mahal" Na Rufe Ciki.
Post Top Ad
| Latest News | Entertainment | Seince & Technology |Advertisement |Videos| Books | Love Quate & Others |
Wednesday, 19 December 2018
Shin Ko Kunsan Mene Ginin "Taj-Mahal-?
Tags
Famous#
Share This

About Najib Muhammad Ya'u Ja'en
Famous
Tags
Famous
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Post Top Ad
Your Ad Spot
Author Details
My Name Is Najib Muhammad Ya'u,I Live In Ja'en Yamma Kano Nigeria,For More Infor Find Me On This Number 08168211346,Thank You.
Masarrafar Antaya Labarai
Breaking News From World Wild
No comments:
Post a Comment
Comment