Mala Singha
Mala Sinha.Biography
An haifi wannan jaruma a ranar 11 ga watan Nuwamba (November) Wanda yai daidai da watan da aka haifi jarumi Sharukhan kenan. Jarumar an haifeta a shekarar 1936 kuma ta kasance tsohuwar Jaruma wacce tayi aiki a yaruka daban daban wanda suka hadar da Hindi, Bengali da kuma Nepal. Jarumar an Santa sosai a bangaren kyau da kuma Kasancewa Babbar Jaruma da ake tunqaho dasu a qarni na 1950s, 1960s Kai harda ma qarni na 1970s a Hindi Cinema. Jaruma tayi finafinai wayanda yawan su yakai kimanin Ko kuma ince Fiyeda Guda 100 . Acikin finafinan da tayi akwai irinsu (pyaasa) a shekara ta alif 1957 (Anpadh) a shekarar alif (1962) Dil Tera Deewana a shekara ta alif (1962) (Gumrah) a shekara ta alif 1963 (Bahurani) shima duka a shekara ta alif 1963 Gehra Daag, Apne Huye Paaraye, Jahan Amara, Himalaya Ki main God duka a shekarar alif 1965, Nai Roshni A shekara ta alif 1967 (Ankhen) a shekara ta alif 1968 (Maryada) 1971 Da kuma babu a shekara ta alif 1985.
Jaruma Mala Sinha ta futo a finafinai da manyan jarumai irinsu Dharmendra, Raaj Kumar, Rajendra Kumar, Biswajit, Kishore Kumar, Manoj Kumar Da kuma jarumi Rajesh Khanna. Taxama Jaruma mafi daukar kudi a film a qarni na 1958s-65 da Vyjanthimala, sannan taqara zama mafi biyan kudi (most high paid actress) daga shekara ta alif 1966-67.
Jaruma Mala Sinha an haifeta acikin dangin Nepali, babanta Sunanshi Albert Sinha Kuma yakasance dan addinin Kirista (Christianity) . Farkon sunan Jaruma Mala Sinha shine Alda, abokanan ta kuma a makaranta suna kiranta da (Dalda) a India Dalda yana nufin (abinda yashafi man vegetables), so jaruma Mala Sinha ta chanja Sunanta zuwa (Baby Nazma) bayan ta samu assignment dinta na farko a matsayin qaramar mawaqiya, bayan ta girma kuma ta qara chanja Sunanta zuwa Mala Sinha. Sanda tana yarinya, ta koyi rawa da waqa Duk da an shigar da ita a kowanne gidan Radio dake qasar India. Bata taba rera waqa a film ba. A matsayinta na mawaqiya, takai matakai daban daban daga shekara ta alif 1947 zuwa 1975.
Jaruma Mala Sinha career ta tafara a qaramar mawaqiya a finafinan Bengali irinsu Jai Vishno, Noted : Mai bada umarni a Bengali mai suna Ardhendhu yaga acting dinta a makaranta ne shine ya nemi ixinin iyayenta da zai sakata a shirinsa mai taken (Roshanara) a shekara ta alif 1952 wanda yakasance shine shirinta da tafara futowa a matsayin Jaruma.
Kasance dani a yau da misalin qarfe 9:30 tonight domin jin yanda Jaruma Mala Sinha tashigo Bollywood.
By Auwal Isah Prabhas.
No comments:
Post a Comment
Comment