Prabhas
Yayinda Ss Rajamouli yake shirye shiryen aikin shirinsa mai taken Rrr wanda yahada manyan jarumai irinsu jarumi Mega Ram Charan da kuma Young Tiger Nandamuri Taraka Rama Rao acikin shirin, Toh a yanxun haka labari da yake xuwar shafin Zauren India ya tabbatar da cewar babban jarumin yankin na Telegu zai zama babban baqo a wajen taron gabatar da shirin. Taron wanda aka za'a gabatar dashi a ranar 11th Nuwamba (November) shekarar dubu 2018 wacce muke ciki. Tabbas Mashiryin shirin da sauran masu ruwa da tsaki na shirin sune sukeso jarumin yakasance babban baqo a wamen taron. # DVV Entertainment da Ss Rajamouli sune Mashirya shirin A yanxun haka suna jiran amincewar jarumin Bahubali akan halartar taron da za'ayi.
Shirin wanda yasamu kasafin kudi kimanin 300 Crore Rs, shirin yasamu hadin kan Gwarazan jarumai da suke daya daga cikin jarumai wayanda sukeda stardom a yankin Telegu Irinsu jarumi JR NTR ya kuma Mega Star Ram Charan duka acikin qayataccen shirin a karo na farko haduwarsu. Wannan shine karo na 3 da jarumi JR NTR suka hada shiri da mashiryin shirin Ss Rajamouli.
Shirin yakasance labarine a shekara ta alif 1920,yayinda shirin yasamu labari daga hannun 'KV VIJAYENDRA Prasad' yayinda MM Keravani shine ya shirya waqar shirin.
Vijaeyandara Prasad yakasance marubucin shirin kuma yakasance uba ga Ss Rajamouli, kuma kowa yasan wanene Vijeyandra Prasad indai wajen kawo labarine Mai kyau. A yanxun haka jarumi Ram Charan yana kan aikinsa na RC 12 wanda 'Boyapati Srinu' yake bada umarnin shirin.
Tuni jarumi JR NTR yafara aikin shirin na RRR a yayinda Lloyd Stevens yafara bashi Training na musamman domin tunakarar shirin.
Report By : Auwal Prabhas.
No comments:
Post a Comment
Comment