Fadar Masoya
Samfurin Kalaman Soyayya
Masoyiyata, ina son ki fiye da yadda kike so na.
Ina son kasancewa tare da ke domin kina
farantawa zuciyata.
Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari, duk
wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Ke ce farin
cikina. Ina nan riƙe da amanar soyayyarki har
ƙarshen rayuwata. Na saka a raina ba zan taɓa
mantawa da ke ba.
Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke
ƙawatu wa da kallonsa, hanci ya ji daddaɗan
ƙamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan
rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba,
haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba.
Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a
tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin
zuciyata.
Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi
da furannin da suke lambun zuciyata.
No comments:
Post a Comment
Comment